Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama yana Korea ta kudu domin halartaron taron kolin makaman nukiliya


Taron kolin nukiliya

Jiya lahadi shugaba Obama na Amirka ya isa kasar Korea ta kudu domin halartar taron kolin nukiliya da za’a fara gobe litinin idan Allah ya kaimu.

Jiya lahadi shugaba Barack Obama na Amirka ya ziyarci sojojin Amirka wadanda suke gadin yankin da ba’a harkokin soja a cikinsa daya raba kasashen Korea guda biyu, ya kuma gaya musu cewa sun taimakawa kasar Korea ta arewa samun ci gaba.

Jiya lahadi shugaba Obama na Amirka ya isa kasar Korea ta kudu domin halartar taron kolin nukiliya da za’a fara gobe litinin idan Allah ya kaimu.

Da sanyin safiya ya sauka a sansanin mayakan saman Amirka dake birnin Seoul, kuma ana sa ra wani lokaci a yau din zai gana da shugaban Korea ta kudu Lee Myung Bak.

Ana kuma sa ran sanarwar da Korea ta arewa ta bayar na shirin harba watan dan Adama akan makami mai linzami mai cin dogon zango a watan gobe zai kanainaiye taron kolin wanda fiye da shugabanin kasashe hamsin zasu halarta.

Majalisar Dinkin Duniya da Amirka da kungiyar kasashen turai da Rasha da kuma Japan, duk sun yiwa Korea ta arewa kashedin cewa wannan shiri nata ya keta ka'idodin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya, a saboda haka tayi watsi da shirin. Hatta China kawar Korea ta arewa, itama ta baiyana damuwa tana mai fadin cewa harban rokan zai dagula kwanciyar hankali a yankin.

XS
SM
MD
LG