Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Trump Ya Amince da Tillerson, Sakataren Harkokin Wajen Kasar


Donald Trump, shugaban Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana amincewarsa da Rex Tillerson sakataren harkokin wajen kasarsa bayan da ya musanta abun da wata jarida ta kwarmata cewa yana shirin barin gwamnatin Trump saboda rashin jituwa tsakaninsu

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cikakkiyar amincewarsa da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, sa’o’i bayan bullar wani labari da ya warwatsu a duniya mai nuna cewa akwai takun tsaka tsakanin su biyun.

Shugaba Trump yana magana ne bayan da ya ziyarci wani asibiti a birnin Las Vegas na jihar Nevada, domin jajantawa mutanen da harbin Las Vegas ya shafa kuma yayi kalaman nasa ne ‘yan sa’o’i bayanda sakatare Tillerson ya fito, yana musunta rahotan da ke cewa yana gaf da ajiye aikinsa.

Bayan da ya jero wasu nasarori da yace shugaba Trump da ministocinsa sun cimma a fannin diplomasiya, wanda ya kwatanta da cewa yin aiki tare ne yasa aka kai ga nasarar, Tillerson ya musanta cewa yana ya kusa ajiye aikinsa a watan Yuli.

Da yake magana da manema labarai, Tillerson ya ce mataimakin shugaban kasa, Mike Pence, bai taba lallabarsa ba ya ci gaba da rike aikinsa ba, saboda bai taba tunanin barin aikin nasa ba.

Sakatare Tillerson dai yayi magana ne a jiya Laraba gaban manema labarai, ranar kuma da gidan talabijin na NBC ya fitar da rahotan da ke cewa ya kusa yin murabus a farkon wannan shekarar, bayan kwashe watanni yana famar zama da aiki da shugaba Trump, kuma ya ci gaba ne kawai bayan lallabar mataimakin shugaban kasa Mike Pence.

Haka kuma rahotan na NBC yace Tillerson ya kira shugaba Trump marar hankali wani taro da sukayi da wasu manyan jami’an kasar a ma’aikatar tsaro ta Pentagon.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG