An rawaito cewa shugaban Amurka Donald Trump ya umarci tsohon lauyansa ya yi wa ‘yan majalisa karya akan kokarinsa na son gina otel din Trump Tower a birnin Moscow.
A jiya Alhamis wata karfar sadarwa ta yanar gizo da ake kira BuzzFeed News, ta rawaito cewa rahoton ya fito daga wasu mutum biyu daga hukumar bincike ta FBI wadanda ba’a san ko su waye ba, akan Shugaban Amurka da Tsohon lauyan sa Micheal Cohen.
Majiyar ta ce, Cohen ya fadawa masu bincike na musamman na Robert Mueller, cewa shugaban ya fada masa ya yi wa ‘yan majalisa karya akan mu’amalolinsa da kasar Rasha.
BuzzFeed ta ce masu binciken wadanda ba’a san ko su waye ba, su ma suna cikin wannan binciken.
A cewar kafar yada labaran ta BuzzFeed, shugaba Trump da ‘ya’yansa biyu, Ivanka da Donald karami, suna samun bayanai filla – filla akan ginin, daga Cohen, wanda suka saka a matsayin mai kula da aikin.
A daya gefen kuma, daya daga cikin lauyoyin shugaba Trump, Rudy Giuliani, ya ce mai yiwuwa wasu daga cikin jami’an kwamitin yakin neman zaben Trump a 2016, sun hada kai da Rasha domin su taimaka mai ya samu nasara, amma ya ce sun yi hakan ne ba tare da sanin shugaba Trump ba.
Facebook Forum