Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama Ya Kai Ziyara Burma


Shugaban Amurka Obama A Kan Hanyarsu zuwa Asiya
Shugaban Amurka Obama A Kan Hanyarsu zuwa Asiya
Shugaban Amurka Barack Obama ya isa kasar Burma ya kasance shugaban Amurka mai ci na farko da ya ziyarci kasar dake kudu maso gabashin Asiya.

Mr. Obama zai gana da takwaransa na kasar Burma Thein Sein da kuma Aung San Suu Kyi, babbar ‘yar gwaggwarmayar rajin damokaradiya ta kasar, wadda aka saki a shekara ta dubu biyu da goma bayan ta shafe shekaru 15 karkashin daurin talala.

Shugaba Obama yace ziyarar da zai kai kasar Burma ba yana nufin yana goyon bayan gwamnatin bane, sai dai nuna na’am da garambawul da ake yi a tsarin siyasar kasar.

Mr. Obama yace an nuna niyar yin garambawul a harkokin siyasar kasar Burma saboda haka ya kamata a karfafa masu guiwa.

Yace gurin ziyar tasa ita ce ya nuna irin cin gaban da aka samu, da kuma tattaunawa a kan matakan da ya kamata Burma ta dauka nan gaba.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG