Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama Zai Je Ta'aziya Newtown


Jami'in dan sanda Lt. J. Paul Vance na jihar Connecticut yana jawabi ga manema labarai
Shugaban Amurka Barack Obama zai je garin Newtown na jihar Connecticut domin gaisuwar ta’aziya a garin dake makokin kananan yara 20 da malamai shida da aka kashe.

Sanarwar da fadar White House ta bayar jiya asabar tace Mr. Obama zai gana da dangi da kaunatattun mamatan a makarantar firamare ta Sandy Hook, inda zai kuma godewa wadanda suka fara kai agaji. Sanarwar ta kuma bayyana cewa, shugaban kasar zai yi jawabi a wani taron zaman makoki da za a gudanar domin tunawa da dangi da mamatan da kuma iyalan makarantar.

An bada sanarwar Fadar shugaban kasa ta White House ne ‘yan sa’aoi bayanda rundunar ‘yan sandan jihar Connecticut ta fitar da jerin sunayen wadanda suka mutu ta kuma yi kira ga manema labarai kada su matsawa dangin mamatan da neman bayanai. Jerin sunayen sun kunshi kananan yara ‘yan mata 12 da maza takwas dukansu tsakanin shekaru 6 da 7, ‘yan aji daya. Sauran manyan mutanen shida da aka kashe kuma duka mata ne.

Babban jami’in aikin gwajin jinya na jihar H. Wayne Carver yace ma’aikatansa sun kwana suna aikin tantance dalilan mutuwar mutanen. Yace an harbe su duka fiye da sau daya da doguwar bindigar da aka bayyana tun farko da suna Bushmaster AR-15.
XS
SM
MD
LG