Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Da Shugaban Rasha Na Shirin Ganawa


Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Amurka Donald Trump

Ana shirin wata ganawa tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Rasha Vladimir Putin, a cewar jami'an Fadar White House.

Rahotannin kafafen labarai sun ruwaito wasu majiyoyin da aka sakaya su na cewa ana sa ran ganawar ta faru a watan gobe lokacin da Trump ya kai ziyara Turai. Shugabannin biyu na iya ganawa gabanin taron da za’a yi a Brussels daga 11 zuwa 12 ga watan Yuni, ko kuma bayan ziyarar Trump zuwa Burtaniya kwanaki biyu bayan nan.

Mai magana da yawun Majalisar Tsaron kasa Garrett Marquis ya aika da sako ta kafar twitter ranar Alhamis mai cewa, "Ranar 25 zuwa 27 ga watan Yuni, Mai bayar da Shawara Kan Harkokin Tsaron John Bolton zai gana da kawayen Amurka a London da Rome don su tattauna kan kalubalen tsaro, daga nan kuma ya wuce birnin Mascow na kasar Rasha don tattaunawa kan shirin ganawa tsakanin Shugaba Trump da Putin."

Facebook Forum

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG