Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Donald Trump Ya Kai Ziyara Tsibirin Puerto Rico da Guguwar Maria ta Rugurguza


Shugaban Amurka Donald Trump a Perto Rico

Shugaban Amurka Donald Trump ya kai ziyarar gani da idanunsa irin mugun barnar da guguwar Maria ta yiwa tsibirin Perto Rico wanda ya kasance mallakar Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya je ganewa idonsa irin barnar da guguwa ta yi a yankin Puerto Rico, inda ya gana da shugabannin tsibirin, ciki har da wadanda suka caccaki hukumomin Washington da kakkausan lafazi, kan yadda suka tunkari bala’in guguwar.

Shugaba Trump ya yi amfani da wannan ziyara, wajen yaba matakan da hukumomin tarayyar da sojoji suka dauka, wadanda wasu suka ce sun yi kadan kuma an yi jinkiri wajen daukansu, domin ceto rayuwar jama’ar da guguwar ta shafa,

Kebabbun wuraren da suka fuskanci bala’in guguwar, sun yi fama da matsalar rashin ruwa da sauran ababan more rayuwa har na tsawon sama da mako guda.

Jim kadan bayan da shugaban Amurkan ya kammala ziyarar tasa, hukumomin yankin na Puerto Rico suka bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu ya haura daga 16 zuwa 34.

A baya Trump ya kwatanta kisan da wannan guguwar ta yi da ta Katrina wacce ta halaka mutane sama da1800 a New Orleans a shekarar 2005, inda ya ce babu hadi da ta Katrina wacce ta halaka dumbin jama’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG