Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Na Jin Ganawa Da Shugaban Koriya ta Arewa Kamar Almara


Frank Salazar, 70, shows an 'I voted' sticker after casting his ballot on the Super Tuesday, at a voting center in Alhambra, Calif., March 3, 2020.
Frank Salazar, 70, shows an 'I voted' sticker after casting his ballot on the Super Tuesday, at a voting center in Alhambra, Calif., March 3, 2020.

Shugaban Amurka Donald Trump na jin ganawa da shugaban koriya ta Arewa a yankin dake tsakanin koriyoyin biyu inda aka hana ayyukan harkokin soji kamar almara ce, wato abun mamaki da watakila ma ba zata faru ba.

Ganawa da shugaban Koriyaa ta Arewa a yankin nan da aka hana harkokin soji,akan iyakan koriyoyin biyu zai kasance "da mamaki" inji shugaban Amurka Donald Trump, yana fadawa manema labarai a jiya Litinin, sa’o’I bayan sakon tweeter da ya aike a kan taron kolin da yake shirin yi da Kim Jong Un a ginin da ake kira "Peace House ko Freedom House" dake kan iyakar Koriya ta Arewa da ta Kudu.

Yace muna nazari a kan gudanar da taron a kasashe da dama ciki har da Singapore kana muna tattaunawa a kan yiwuwar yin taron akan iyakokin kasashen biyu inda aka hana harkokin soja, kamar yadda shugaba Trump ya fada a lokacin da ya gana da manema labarai tare da shugaban Najeirya Muhammadu Buhari a fadar White House.
Shugaban na Amurka yaki ya bayyana wasu wuraren da za a iya gudanar taron baicin Singapore da akan iyakokin koriyar biyu,Trump yace "labari mai dadi" cikin wannan lamari shine kowa yana so a taron a kasarsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG