Accessibility links

Shugaban Amurka ya bayyana goyon bayan kwamandan kasar a Afghanistan


John Allen

Kakakin fadar White Jay Carney yace shugaba Barack Obama yana ci gaba da baiwa janar John Allen cikakken goyon baya a ci gaba da aikinsa na kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan, yayinda ake gudanarda bincike kan kwamandan bisa zargin “cudanya ko magana da ta kaucewa ka’ida” da wata mace, wacce take tsakiyar abin fallasan nan da ya kai ga darektan hukumar CIA David Petreaus, yin murabus.

Kakakin fadar White House din yace Mr. Obama yana ganin kimar Janar Allen da kuma irin yadda yake bautawa Amurka.

Tunda farko shugaban Amurkan ya dakatarda zaben Janar Allen ya zama kwamandan rundunar tsaro ta NATO har sai ma’aikatar tsaron Amurka ta kammala bincike da take yi akansa. Wata daya daya shige ne shugaban Amurkan ya zabi Janar John Allen ya zama kwamandan NATO.

Zargin da ake yiwa janar Allen ya shafi musayar wasiku da Jill Kelly, wacce aka bayyana ta a matsayin kawa ga Petreaus da iyalinsa. Korafin da Jill Kelly ta gabatar wa hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka watau FBI, game da wasiku ta email masu barazana, daga matar da janar Petreaus yayi lalata da ita, itace dai matar da kuma ta rubuta littafi kan tarihin rayuwar Petreaus din, lamari da ya kai Janar din mai ritaya yin murabus daga mukaminsa na Darektan hukumar CIA.
XS
SM
MD
LG