Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Yi Kira A Kawo Karshen Tsaurin Ra'ayi


Shugaba Obama yana jawabi a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya su yi allah wadai da kakkausan lafazi kan tashin hankali da kuma tsaurin ra’ayi, yace duniya zata ci gaba ne kawai ta wajen kai zuciya nesa da kuma ‘yanci.

Mr. Obama ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa a taron koli na 67 na Majalisar Dinkin Duniya, inda aka rika tafa masa. Ya shaidawa mahalarta taron cewa, “lokaci ya yi na maida wadanda suke nuna kiyayyarsu ga Amuraka da kuma kasashen yammaci wajen tada hankali.

Jawabin nasa ya maida hankali kan zanga zangar da aka shafe makonni ana gudanarwa na nuna kyamar silman batanci kan addinin Islama da aka harhada a Amurka. Mr. Obama ya bayyana bidiyon a matsayin mai ban kyama, sai dai yace wannan bai zama hujjar zubar da jinin wadanda basu ci ba, basu sha ba, da suka hada da jakaden Amurka a Libya Chris Stevens wanda aka kashe a wani harin da aka kai ofishin jakadancin Amurka a Benghazi.

Mr. Obama ya ci alwashin cewa, Amurka zata yi farautar wadanda suka kashe shi ta kuma hukumta su.

Shugaban Amurka ya kuma yi magana da kakkausan lafazi kan shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad, tare da bayyana gwamnatin a matsayin “gwamnatin dake kuntatawa kananan yara da harba roka kan gidajaen kwana.”

Ya kuma gargadi Iran da cewa, Amurka “zata yi dukan abinda ya wajaba” na hana Tehran mallakar makaman nukiliya. Yace har yanzu akwai damar tattaunawa dangane da batun ayyukan Iran na nukiliya sai dai, “lokaci yana kurewa.”
XS
SM
MD
LG