Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban asusun IMF yayi murabus


Shugaban IMF Dominique Strauss-Kahn
Shugaban IMF Dominique Strauss-Kahn

Shugaban asusun IMF Dominique Strauss-Kahn yayi murabus daga mukaminsa bayan da aka kama shi a saboda zarge zargen yin lalata da wata. Yanzu haka dai ana tsare da tsohon shugaban na asusun IMF a wani gidan yari a birnin New York.

Shugaban asusun IMF Dominique Strauss-Kahn yayi murabus daga mukaminsa bayan da aka kama shi a saboda zarge zargen yin lalata da wata. Yanzu haka dai ana tsare da tsohon shugaban na asusun IMF a wani gidan yari a birnin New York. Yace yana son ya maida hankalinsa sosai wajen wanke kansa da zargin da ake yi masa. Murabus din da Strauss-Kahn yayi, ya tado muhawara akan wanda zai maye gurbinsa. Bisa al’ada dai, shugaban asusun IMF yana fitowa ne daga wata kasar turai karkashin wata yarjejeniyar data tanadi, ba-Amerike ya zama shugaban bankin duniya. Jami’an turai sunce asusun IMF yana taka muhimmiyar rawa wajen magance rikicin basussukan kasashen turai, a saboda haka yana da muhimmanci shugaban asusun na gaba, ya zama wanda yake da masaniya sosai akan batutuwan kasashen turai. Rahotanin sun baiyana cewa akwai masu kwadayin wannan mukami daga kasashen Indiya da Singapore da Turkiya da Afrika ta kudu da kuma wasu kasashe.

XS
SM
MD
LG