Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jagoran Binciken Katsalanda A Zaben 2016 Zai Yiwa Shugaba Trump Tambayoyi


Robert Mueller

Binciken da hukumar da Robert Mueller yake yiwa jagoranci take gudanarwa ya kawo gaban goshi saboda lauyoyin shugaba Trump sun gana da kwamitin da zummar sanin yadda za'a yiwa shugaban kasa tambayoyi

Mai bincike na mussaman akan zargin shishigin da aka ce Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016 ya gana da Lauyoyin da ke wakiltar shugaba Donald Trump akan yin hira da shugaba Trump.

Bangarorin biyu sun gana a watan da ya gabata , amma mutanen da ke da masaniya ko fahimta akan lamarin basu bada bayani ko za’a yi hirar ba.

Tsohon darectan FBI, hukumar dake binciken manyan laifuka, Robert Mueller, na ta yin binciken wata da watanni da ya yi sanadin tuhumar mutane hudu, ciki har da wani wanda ya taba yi wa Trump manajan kamfe Paul Manafort da tsohon mai bada shawara akan harkokin tsaro, Michel Flynn.

Masu binciki na duba ko Shugaba Trump ya nemi lalata binciken FBI bayan da ya kori tsohon darektan hukumar ta FBI, James Comey, daga aiki

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG