Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Koma Najeriya


Shugaba Buhari, bayan ya sauko daga jirgi
Shugaba Buhari, bayan ya sauko daga jirgi

Bayan ya kwashe kwanaki 51 yana hutu tare da yin jinya a Ingila, da safiyar yau Juma'a shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sauka a garin Kaduna daga birnin London.

Yayin da shugaba Muhammad Buhari ya sauka a garin Kaduna 'yan jarida da suka kwashe sa'o'i da dama suna dakon dawowarsa ba su samu tattaunawa da shi ba saboda jami'an tsaro sun kankange duk hanyoyin da za su bi su yi masa tambayoyi.

To sai dai jim kadan bayan tawagar gwamnatin jihar Kaduna ta raka shugaban zuwa shiga jirgi mai saukar anugulu da zai kaishi Abuja, manema labarai sun nemi jin ta bakin mataimakin gwamnan Kaduna Barnabas Bala Bantek game da dawowar shugaban kasar.

Dawowar Shugaba Buhari
Dawowar Shugaba Buhari

A cewar Bala Bantek shugaba Buhari ya tambayesu ina gwamnan jihar ya je kuma yaushe zai dawo.

Da saukan a Kaduna, shugaba Buhari ya dangana da birnin Abuja, inda aka dauke shi a wani jirgi mai saukar ungulu.

Tuni dai labarin dawowar shugaban ya cika garin Kaduna kuma yau ko'ina batun dawowarsa a ke yi.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

Facebook Forum

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG