Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Zai Tattauna Da'Yan Majilisun Kasa


Moldova/U.S. - American Senators (John McCain) at USEM, Chisinau, 17 April 2014.

Shugaban Amurka da wasu Sanatocin jamiyyar su dama 'yanmajilisar zartarwa zasu gudanar da wani taro a Camp David

Shugaba Amurka Donald Trump zai gana da ‘yan jamiyyar su ta Republican dake majilisar dokokin kasar hadi da ‘yan majilsar zartarwan sa.

Zasu yi wannan ganawar ce kuwa a Camp David domin duba muhimmam bartuwan da gwamnatin zata baiwa mahumamci.

Cikin batutuwan da zasu tattauna akai ko sun hada da batun zaben rabin waadi da za a gudanar cikin watan nuwamba.

Shugaba Trump yace zamu tafi Camp David da ‘yan jamiyyar Republican musammam ma manya-manya sanatocin ta, domin ganin mun ciyar da Amurka gaba.

Shugaban yana wannan kalamin ne a dai-dai lokacin da yake barin fadar White House akan hanyar sa ta zuwa wurin wannan taron.

Shima mataimakin shugaban kasa Mike Pence da sauran ministoci da dama zasu halarci wannan taron.

Shugaban dai yana neman Karin waasu nasarori baya ga wanda ya samu na ganin kudirin nan na haraji wanda ya riga ya zame doka.

Wasu daga cikin batutuwan da zasu dauki hankali ko kuma suyi tasiri a wannan taron sun hada da batun kasafin kudi,kayayyakin more rayuwa, jin dadin jamaa,Batun shiga da fice,sai kuma maganar zaben tsakiyar waadi.

Yanzu ya zame wajibi ‘yan majilisar su amince da kudin da za ayi anfani dasu wajen tafiyar da gwamnati daga yanzu zuwa 19 watan nan da muke ciki domin kaucewa wa kulle tafiyar da daukacin ayyukan gwamnati.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG