Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Faransa Ya Soki Lamirin Sojojin Turkiya A Siriya


Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande

Shugaban Faransa Francios Hallande ya soki lamarin ayyukan sojojin Turkiya a arewacin Siriya inda yake cewa sunkai doki masu cin karo da juna da ka iya kara ruruta wutar rikicin.

Hollande ya nanata a yau Talata cewa akwai bukatar gaggauta kawo karshen rikicin Siriya kuma a koma kan teburin tattaunawa.

Kalaman nasa sun zo ne kwana daya bayan da sakataren tsaron Amurka Ashton Carter yayi kira ga Turkiya da su maida hankali wurin yaki da ISIS kuma su daina tada rigima da rundunar Kurdawa masu kawance da Amurka da su kuma suke fafatawa da kungiyar ISIS a Siriya.

XS
SM
MD
LG