Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya


Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00

Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Mali Assimi Goita, ya ce yana cikin koshin lafiya bayan da wani mutum ya yi yunkurin daba masa wuka a babban Masallacin birnin Bamako a ranar Talata yayin da Musulmi ke bukukuwan Babbar Sallah.

“Komai lafiya lau, babu wata damuwa. Shi shugabancin dama ya gaji haka, akan samu mutanen da kan so su haifar da rudani, saboda ba su gamsu da abin da ake yi ba. Wannan lamari ne da tuni aka riga aka shawo kansa. Ina mai tabbatarwa da al’umar kasar nan da na duniya baki daya cewa, lafiyata kalua, babu wata damuwa. Babu kuma wanda ya ji wani rauni. Ina mai kira ga jama’ar kasar Mali da sauran kawayenmu da su ba mu hadin kai.”

XS
SM
MD
LG