Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Hukumar Kwastan Ya Yi Ritaya


Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde,

Shugaban Najeriya ya yi bikin karbar ritayar shugaban hukumar kwastan Abdullahi Dikko Inde

Yau Litinin shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya yi bikin jinjinawa shugaban kwastan din Najeriya Abdullahi Dikko Inde wanda ya yi ritaya yau bayan ya yi shekaru shida yana shugabancin hukumar.

Shugaban kasa ya yabawa Alhaji Inde akan nasarorin da hukumar ta samu lokacin shugabancinsa. A lokacinsa an samu karin kudaden haraji da sauye-sauye na zamani wurin anfani da naurori masu kwakwalwa.

Wadannan naurorin sun inganta hukumar idan aka kwatantata da sauran takwarorinta na duniya. Shugaban ya yi masa fatan alheri akan ayyukan da zai yi nan gaba.

Inde yace kafin ya rubuta takardar ritaya ya zanna da shugaban kasa. Bayan ya fahimci abubuwan da shugaban kwastan din ya yi ya yaba masa. Ya umurceshi ya rubuta aniyarsa na cewa shi ne ya kuduri aniyar barin aiki ba awai an koreshi ba ne.

Ga karin bayani

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG