Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ivory Coast Ya Kori Shugabannin Jami'an Tsaron Kasar


A girl poses for a photo during a visit to the Instagram museum "Smile Safari" that recently opened in Brussels, Belgium.

Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast ya kori babban hafsan hafsoshin kasar, na rundunar'Yansanda da rundunar jandarmomi, bayan wani bori da wasu jami'an tsaro suka yi a duk fadin kasar.

A wata sanarwa daga fadar shugaban kasa da aka karanta jiya Litinin a talabijin, tace an kori babban hafsan hafsoshi Janar Souma'ila Bakayoko, wanda yake ci gaba da zama marasa farin jini tsakani sojoji,haka nan na'ibinsa ma Janar Sekou Toure an yi awon gaba da shi. Haka nan shugaban kasar ya sallami babban kwamandan rundunar Jandarmomi Gervais Kouakou Koussai, da kuma speto janar na 'Yansandan kasar Bredou M'bia.

Haka nan a jiya Litinin, Firayim Ministan kasar Daniel Kablan Duncan yayi murabus, ya kuma rusa gwamnati, mataki da aka so a dauka bayan da aka gudanar zaben 'yan majalisa cikin watan jiya, amma aka jinkirta shi da wasu kwanaki saboda borin da sojojin suka yi a fadin kasar a karshen makon jiya.

An fara borin ne ranar Jumma'a da ta shige,lokacinda sojojin suka kama Bourke, birni na biyu a girma cikin kasar, suka nemi a biya alawus alawus dinsu da kuma karin albashi. Daga bisani borin ya bazu zuwa sauran sansanonin sojoji dake fadin kasar.

An kawo karshen borin ne bayan da gwamnati ta bada kai bori ya hau a ranar Lahadi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG