Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Jamhuriyar Nijar Ya Yiwa Gwamnatinsa Gyaran Fuska


Shugaban Nijar Issoufou Mahammadou

Wata sanarwa da sakataren gwamnatin kasar Nijar ya fitar ta ce shugaba Issoufou Mahammadou ya sallami wasu ministocinsa da zummar maye gurbinsu da wasu sabbi

Jiya Litinin ne sakataren gwamnatin Jamhuriyar Nijar ya bada sanarwar cewa shugaban kasar ya yiwa gwamnatinsa garambawul kuma ya maye gurbin wadanda ya sallama da wasu sabbabi.

A gyarar fuskar da aka yi, Yusufu Katambe zai maye gurbin Barmo Salifu da aka sallama daga mukamin ministan albarkatun ruwa yayinda Mammadou Karijo ya maye gurbin ministan sufuri Laren Tana. Da ma tuni ake rade-radin ministan sufurin zai fice daga gwamnati sanadiyar tabarbarewar dangantaka tsakanin jam’iyyarsa ta Amin Amin da PNDS mai mulki.

Ita ma Kiristani Rakiyatu Jaku da yanzu ta fice daga gwamnatin, ‘yan jarida sun yi hasashen zata fice saboda rashin jituwa da ya kunno kai tsakaninta da Firayim Ministan Kasar, Birji Rafini, game da cancantar gudanar da wani aiki na Bankin Duniya. To sai dai zata koma ma’aikatar kwadago.

Tun a watan Agustan da ya gabata ne masu rajin kare dimukradiya da wasu ‘yan kasar suka dinga kiran Shugaba Issoufou ya yiwa gwamnatinsa garambawul da zummar takaita yawan ministocinsa su 43 domin a rage kashe kudi a kasar dake fama da fatara.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:37 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG