Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kamfanin Volkswagen Ya Yi Murabus


Martin Winterkom shugaban kamfanin volkswagen da ya yi murabus

Kamafanin Volkswagen ya shiga wata badakala biyp bayan aikata rashin gaskiya da nufin kawar da hankalin mahukunta da kuma cutar kwastamomi lamarin da yanzu sun fara mutane sun dakatar da sayan motocin kamfanin

A jiya Laraba, shugaban kamfanin kera motar Volkswagen Martin Winterkorn ya ajiye aikinsa, a daidai lokacin da ake kan badakalar kamfanin Jamusawan.

Game da yadda kamfanin ya yi kumbiya-kumbiyar kaucewa kula da yawan motocin da zasu kera har guda Miliyan 11, don kaucewa gwajin gurbatar yanayi.

Winterkorn yace, ya dauki alhakin laifin matsalolin da aka gano a injin motocin, amma yace bashi da masaniya game da wani aikata ba daidai ba. Yace kamfanin na bukatar sabon yanayin fara aiki da kuma ma’aikata.

A cewarsa, murabus dinsa zai bada wannan dama. Ya yi kira ga kamfanin da su ci gaba da aiwatar da tsarin aiki a bisa tantancewa kuma a bayyane.

XS
SM
MD
LG