Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kungiyar ISIL ya yiwa Kayla Mueller fyade


Mariganyiya Kayla Mueller

Kafofin yadda labarun Amirka sun yayata cewa wata ma'aikaciyar agaji BaAmerikiya mai suna Kayla Mueller da aka kashe kimamin shekara guda a lokacinda take hannun yan yaki sa kan kungiyar ISIL, shugaban kungiyar ISIS din yayi mata fyade kafin mutuwar ta.

Kafofin yadda labarun Amirka sun yayata rahotanin cewa wata ma'aikaciyar agaji BaAmerikiya mai suna Kayla Mueller da aka kashe kimamin shekara guda a lokacinda take hannun yan yaki nsa kan kungiyar ISIS, shugaban kungiyar ISIS din yayi mata fyade kafin mutuwar ta.


Kafofin yada labaru sun ambaci jami'an dakile ta'adanci da kuma zantawa da iyayen Kayla wadanda suka tabbatar cewa a watan Yuni jami'an Amirka suka fada musu cewa shugaban kungiyar ISIS Abu Bakr Al Baghdadi ya yi lalata da yarsu.


Gidan Talibijin na ABC ne ya fara bada rahoton fyaden da aka yiwa Kayla, kuma ya ambaci iyayen Kayla Carl da Marsha suna fadin cewa an musgunawa yarsu kuma Al Baghdadi yayi yadda yaga dama da ita. Gidan talibijin na ABC yace Al Baghdadi ya yi wa Kayla fyade a gidan Abi Sayyaf wanda sojojin kundubalan Amirka suka kashe shi a farkon wannan shekara a gidansa.


An samu wannan labarin ne daga wasu kafofi, ciki harda wasu 'yan mata guda biyu wadanda suma suka yi zargin cewa an yi musu fyade a gidan Abu Sayaf kafin suka samu nasarar arcewa.
A watan Augustan shekara ta dubu biyu da goma sha uku yan ISIS suka kama Kayla a Aleppo dake arewacin Syria, kuma yan kungiyar ISIS sun tsare ta har na tsawon watani goma sha takwas.


Kungiyar ISIS tayi ikirarin cewa an kashe Kayla ne a watan Fabrairu lokacinda kasar Jordan ta kai musu hare hare da jiragen saman yaki. To amma tunda farko jami'an Amirka sun yi tababan yadda aka kashe Kayla.

XS
SM
MD
LG