Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Ya Koma PDP


Bukola Saraki A Wata Tattaunawa Da Reuters
Bukola Saraki A Wata Tattaunawa Da Reuters

Shugaban majalisar dattijan Najeriya Abubakar Bukola Saraki ya sanar da ficewa daga jam'iyar APC mai mulki ya koma babbar jam'iyar hamayya PDP.

Shugaban majalisar dattijan ya buga a shafinsa na twitter cewa, "ina so in sanar da 'yan Najeriya cewa, bayan kyakkyawar tuntuba na yanke shawarar barin jam'iyar APC.

Bukola Saraki, ya bayyana cewa, yana la'akari da cewa, alhakin dubban mutane ya taraya a wuyansa da suka hada da magoya bayansa da abokan arziki da na siyasa da suke dogara ga jagorancinsa, sai dai tura ta kai bango kasancewa duk wani yunkurin sulhu da zaman lafiya da kuma ci gaban da suke nema ya cimma tura.

An jima ana radi radin cewa, shugaban majalisar dattijan yana shirin sake sheka bayan jimawa suna takun saka da wadansu jami'an gwamnati.

Tuni jam'iyar PDP da kuma wadansu kusoshi a jam'iyar da suka hada da tsohon mataimakin Najeriya Atiku Abubakar da ya bayyana niyar tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin tutar jam'Iyar PDP suka yaba matakin da shugaban majalisar dattijan ya dauka.

Zamu ci gaba da kawo maku ci gaban da aka samu kan wannan batu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG