Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa Ya Tsallake Rijiya da Baya


Dakin Majalisar Jihar Adamawa

Guguwar tsige-tsige da ta ratsa majalisar dokokin jihar Adamawa ta rutsa da duk shugabaninta sai kakakin majalisar Kairu Mijinyawa da ya sha da kyar

A zaman majalisar a wannan Litinin kakakin majalisar wanda ya jagoranci zaman majalisar, Kabiru Mijinyawa, ya tsallake rijiya da baya,a guguwar tsigau din ,to amma kuma mataimakinsa Sunday Peter da sauran shugabanin majalisar basu taki sa’a ba, inda yan majalisa 17 cikin 25 suka kada kuri’ar tsige su.

Cikin dai wadanda suka rasa kujerun nasu baya ga mataimakin kakakin majalisar sun hada da shugaban masu rinjaye,da mataimakinsa,da na marasa rinjaye da gagara badau din majalisar.

To wai ko me yayi zafi da yan majalisar suka dauki wannan mataki a yanzu? Hon.Hassan Barguma shine sabon shugaban masu rinjaye na majalisar ya bayyana dalilansu na daukan wannan matakin tsigewan inda yace sun dau matakin ne don kawo gyara.

To sai dai tuni wannan sauyi ya soma jawo cecekuce inda wasu ke zargin cewa da hannun bangaren zartaswa a wannan tsigewa,koda yake gwamnan jihar Sen.Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ya musanta zargin cewa da hannunsa a wannan satoka-sa-katsin.

Gwamnan ta bakin daya daga cikin hadimansa ta fuskar harkokin yada labarai Danjuma Bakari (wato Danjuma Hamas),yace babu hannunsa a ciki.

Suma masana harkar majalisa irinsu Hon.Abdulmumini Ibrahim Song,tsohon dan majalisar dokokin jihar na ganin akwai abun dubawa game da wannan sauyin daya kada a majalisar.

Koma da menene dai yanzu an zura ido a ga yadda zata kaya,yayin da masu fashin baki ke cewa lokaci ne kawai ke iya tabbatar da abun da ka iya faruwa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG