Accessibility links

An Kai Shugaban Mauritaniya Jinya A Faransa


Shugaban kasar Mauritaniya a gadon asibiti

Rahotannin na cewa an dauki shugaba Muhammad Ould Abdel Aziz na kasar Mauritania zuwa wani asibitin kasar Faransa domin duba lafiyarsa, kwana guda bayan harbin bindigar da aka yi masa. Jami’ai sun ce ya dan jikata, kuma anyi harbin ne cikin kuskure.

Anga shugaba Abdel Aziz yana Magana ta kafar gidan Telbijin daga kan gadonsa na Asibitin da yake jiyyar farko kafin a dauke shi zuwa Asibitin birnin Paris. Yace yana samun sauki kuma kada a nuna wata damuwa ba da wata gayya aka harbeshi ba.
XS
SM
MD
LG