Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari Ya Gana da Manyan Hafsoshin Sojojin Kasar cikin Siri


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

A cikin sirri, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya gana da duk manyan hafsoshin sojojin kasar tare da manyan shugabannin ‘yansanda da kuma mai bashi shawara kan harkokin tsaro, abun da masana suka ce yin hakan na kan ka’ida domin lamuran tsaro

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya gana cikin siri da manyan hafsoshin sojojin kasar a fadarsa ta Aso Rock dake Abuja.

Sun kwashe sa’o’i hudu suna ganawa amma daga karshe ba’a bayyanawa ‘yan jarida makasudin taron ba.

To sai dai masana irinsu Farfesa Muhammad Tukur Baba na ganin ganawar na da tasiri ga sha’anin tsaron kasa. Yana mai cewa wajibi ne ma shugaban ya dinga ganawa da jami’an tsaro kowane mako saboda irin yanayin da kasar ke ciki.

Shi kuwa Aliko El-Rashid Haroun, wani tsohon hafsa a rundunar tsaron Najeriya, cewa yake akwai matsaloli da dama kamar ‘yan IPOB masu rajin neman kafa kasar Biafra dake bukatar a rinka maida hankali a kansu, ga kuma matsalar masu garkuwa da mutane.

Shi ma Air Commodore Baba Gamawa yace irin wannan ganawar ta shugabannin ma’aikatun tsaro ba wani sabon abu ba ne. A cewarsa, daga lokaci zuwa lokaci ya kamata shugaban kasa ya dinga zama da jagororin tsaro don a rinka nazarin ci gaban da aka samu da kuma matsalolin da ake fuskanta.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG