Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Ya Ce Kowani Ministansa Zai Rika Yin Aiki


Shugaba Muhammadu Buhari

Yayin da ake ta cece-kuce kan makomar wasu ministoci, Shugaba Buhari ya bayyana cewa babu Ministan da zai yi zaman kashe wando.

Sabanin yadda aka fahimci bayanin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, Shugaban kasar ya bayyana cewa ba haka abin yak e ba; kowa zai yi aiki. Shugaba Buhari ya yi wannan bayannin ne a ganawarsa da sabbin Ministocin da aka tantance.

Da ya ke jawabin bude taron, Shugaba Buhari y ace kowani Ministansa zai zama mai aiki tukuru don ba da tasa gudunmowa wajen farfado da kasar. Daya daga cikin Ministocin mai suna Barrister Solomon Dalung ya tabbatar cewa Shugaba Buhari ya jaddada cewa kowa zai yi aiki.

Barrister Dalung ya ce lallai za a yi Ministoci 36 wadanda ma’aikatatun gwamnati ba za su kai yawansu ba. To amma kowani Minsita zai zama mai aiki ne tukuru – babu wanda zai yi zaman kashe wando.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG