Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Ya Ki Amincewa Da Kara Wa Shugabannin Jam'iyyarsa Wa'adi


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shugaba Muhammad Buhari ya tsaya kan bin tsarin dokokin jam'iyyarsa saboda haka ya ki amincewa da karin wa'adi ma shugabannin, wato yanzu duk wanda yake son ya sake tsayawa zabe sai ya sauka daga mukaminsa wata daya kafin zaben

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ki amincewa da karin wa'adi ga shugabannin jam'iyyarsa ta APC mai mulki bayan wa'adinsu.

Tun farko an amince a kara masu wa'adin shekara daya saboda wa'adinsu zai kare ne a watan Yuni mai zuwa.

Yayinda shugaban ke magana a taron majalisar kolin jam'iyyar ya ce tsarin mulkin jam'iyyar ya yi tanadin duk wanda yake rike da mukami kuma ya na son ya sake tsayawa zabe sai ya bar mukaminsa wata daya kafin zaben.

Shugaba Buhari ya nuna fargaba matuka aka kaucewa tsarin mulkin jam'iyyar saboda duk wani zabe da 'yan rikon kwarya ko wadanda aka karawa wa'adi suka shirya ba zai samu karbuwa ba a doka. Wannan matsayin shugaba Buhari ya kara zaman zullumi a hedkwatar jam'iyyar, da kuma yiwuwar kawar da shugaban jam'iyyar dake kan gado Mr. John Odigi Oyegun wanda baya jituwa da uban jam'iyyar Bola Tinubu.

Yusuf Sallau Mutun Biyu lauya ne mai zaman kansa a Abuja kuma ya yi sharhi akan lamarin. Ya ce kamar dokar kasa dokar APC ma ta ba shugabanninta wa'adin mulki na shekaru hudu. Duk wanda yake son ya sake zama shugaba sai ya sauka wata daya kafin zabe.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG