Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Ya Yi Alkawarin Inganta Rayuwar Al’ummar Niger Delta


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yayinda shugaban Najeriya Muhammad Buhari yake rattaba hannu akan dokar kafa Jami’ar dake nazari akan albarkatun man fetur a Abuja, ya kuduri aniyar inganta rayuwar ‘yan yankin Niger Delta

Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari ya yi alkawari inganta rayuwar al’ummar Niger Delta ta fannoni daban daban.

Shugaban ya ba da tabbacin hakan ne yayinda yake sa hannu a kudurin wata dokar kafa Jami’ar nazari akan albarkatun man fetur da za’a kafa a Effurun dake kusa da Warri a jihar Niger Delta.

A hirar da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa ya yi da wani malamin Jami’a, Dr. Usman Muhammad dangane da mahimmancin jami’ar, malamin yace yana ganin kafa jami’ar a yankin Niger Delta ba zai kwantar masu da hankali ba. A zahiri ma suna iya fitowa da wata fitinar tare da wasu bukatu saboda ta dalilinsu akan yi watsi da cibiyar ilmin man fetur da aka kafa a Kaduna.

Shi ko Farfesa Almustapha Ujudu gani yake wannan sabuwar jami’ar zata rage yawan kashe kudi zuwa kasashen waje neman ilmin.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG