Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum Ya Lashi Takobin Kawo Karshen Matsalar Bara A Kasar


Bazoum Mohamed Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyi masu zaman kansu da shugabanin addinai sun fara jan hankula don ganar da jama’a rashin dacewar bara a matsayin sana’a.

NIAMEY, NIGER - Tuni dai Shugaba Mohamed Bazoum ya ayyana shirin daukan matakai don kawo karshen wannan dabi’a dake bata sunan Nijar a waje.

Mamayar da wasu ‘yan Nijar suka yi wa titunan Dakar na kasar Senegal a makwannin da suka gabata ita ce mafarin dambarwa da ta taso a tsakanin jama’ar wannan kasa dake ganin lokaci ya yi da za a taka burki ga masu fita waje da sunan bara, ganin yadda abin ke wuce gona da iri.

Shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula na Reseau Esperance Bachar Maman na daga cikin masu ciza yatsa akan wannan batu.

Dama daga cikin masu rungumar wannan kaskantacciyar dabi’a na fakewa da addini don mayar da ita sana’a wadan da galibi kan yi abin ba da wata kwakwarar hujja ba, wannan ya sa malamai magada annabawa irinsu Ustaz Malan Haja Alalo suka fara tunatarwa a musulunce.

Wani abinda ke zama bakon al’amari shine irin yadda ake amfani da yara kanana cikin wannan haraka.

Gudunmowar al’umma a yunkurin cire bara daga kawunan wadanda suka mayar da ita sana’a na iya zama wani bangare na matakan murkushe abin tun daga gida.

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum wanda a karshen watan Maris ya bada umurnin maido da wasu ‘yan Nijar sama da 1000 akasarinsu mata da yara dake bara a kasar Senegal ya lashi takobin kawo karshen wannan haraka.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum Ya Lashi Takobin Kawo Karshen Matsalar Bara A Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG