Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Rasha Da Shugaban Ukraine Sun Tattauna Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya


Petro Poroshenko shugaban Ukraine da Vladimir Putin na Rasha
Petro Poroshenko shugaban Ukraine da Vladimir Putin na Rasha

Tattaunawar shuagab Rasha Putin da Shugaban Ukraine Poroshenko nada nasaba da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2015 da suka cimma wadda ba'a bari ta yi aiki ba amma yanzu zasu farfado da ita saboda karuwar tashin hankali

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran aikinsa na Ukraine Petro Poroshenko sun tattauna kan batun aiwatar da 'yarjajjeniyar zaman lafiya ta 2015 wadda ta kasa kawo karshen tashin hankali a gabashin Ukraine, a cewar jaridun kasar ta Rasha.

"Putin ya bayyana damuwa kan karuwar tashin hankali a Donbas da kuma farar hula da dada shiga uku saboda yawan hare-haren da sojojin Ukarain ke kaiwa a yankin," a cewar fadar Kremlin.

A cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta a Minsk a watan Fabrairun 2015 to amma tashin hankali na dada cigaba a yankin, inda mayakan bangarorin biyu su ka saba da yarjajjeniyar tsagaita wutar kulluyaumin.

Shugabannin biyu sun yi magana ta wayar tarho jiya Alhamis, wadda ita ce tattaunawarsu ta biyu cikin makonni biyu da su ka gabata, a cewar kafar labarai ta Rasha, Interfax. Kamfanin dillancin labaran ya ce Poroshenko ya kira Putin ranar 9 ga watan Yuni don su tattauna kan batutuwan jinkai, ciki har da musayar fursuna.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG