Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Rasha Vladimir Putin Zai Iya Kara Neman Takara


Russia
Russia

Majalisar dokokin Rasha ta amince da wani kudurin doka da ya kunshi yin garambawul a kundin tsarin mulkin kasar.

Wannan kudurin dokar zai bai wa shugaba Vladmir Putin damar tsayawa takarar neman wa’adin shugabancin kasar karo na 5.

‘Yan majalisa 160 ne suka kada kuri’ar goyon bayan kudurin a jiya Laraba, yayin da dan majalisa daya ya kada kuri’ar rashin amincewa, ‘yan majalisa 3 kuma basu halarci zaman ba.

Amincewar na zuwa ne sa’o’i bayan da majalisar wakilan kasar ta amince da kudurin dokar a karatun karshe da aka yi masa.

Kakakin majalisar Vyacheslav Volodin, ya shaida wa manema labarai tun da farko cewa, Putin da rukunin ma’aikata na musamman, sun gabatar da bukatun yin garambawul ga tsarin mulki har 390.

Daya daga cikin bukatun na garambawul da majalisar wakilan ta amince shine, za ta shafe dukkan wa’adin mulkin da Putin yayi a baya, wanda zai ba shi damar neman wani sabon wa’adin mulki a shekara ta 2024, bayan karewar wannan wa’adin na mulkinsa.

Wannan dai ya nuna alamun yiwuwar kasancewarsa a kan mulki har ya zuwa shekara ta 2036 idan ya lashe zaben na shekarar 2024, kana kuma aka sake zabensa bayan shekaru 6.

To sai dai wajibi ne sai Kotun tsarin mulki ta amince da duk wani garambawul da za a yi, haka kuma zai zama karbabbe ne kawai idan ya sami amincewar fiye da rabin masu zaben kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG