Shugaban Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan, ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi, nasarar da ta ba shi wani sabon wa’adi, yayin da ofishin shugaban kasa ke ci gaba da samun karin karfin ikon fada a-ji.
Kafar yada labaran gwamnati ta ce, Erdogan ya lashe kashi 53 cikin kashi 100 na kuri’un da aka kada a zaben da aka yi a jiya Lahadi.
Shi kuma Muharrem Ince, na jam’iyyar adawa ta Republican People’s Party (CHP), ya samu kashi 31 cikin 100.
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a a aka jefa a shekarar 2017, ta haifar da sauyi a tsarin siyasar kasar, wanda ya soke ofishin Firai Minista, ya kuma karawa na shugaban kasa karfin ikon sallamar majalisar dokoki, ya kuma nada minisitoci da alkalai.
A wani jawabi da ya yi, shugaba Erdogan ya ce, “alumar kasarsa sun mika mai amanar shugabantar kasar tare da gudanar da ayyuka.”
Facebook Forum