Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Zimbabwe Mugabe Ya Ki Yayi Murabus Jiya Lahadi


Robert Mugabe shugaban Zimbabwe yayinda yake yiwa al'ummar kasar jawabi jiya Lahadi ta kafar talibijan

Yayinda jama'ar kasar ke kyautata zaton shugaban kasar Robert Mugabe zai yi murabus daga mukaminsa jiya Lahadi sai ga shi ya yi kememe har yana cewa shi ne zai jagoranci taron jam'iyyarsu watan gobe

Dadadden Shugaban Zimbabwe Rober Mugabe na fuskantar tsigewa bayan da ya bayyana karara a wani jawabi ta kafar talabijin cewa ba fa zai sauka ba,

Miliyoyin ‘yan kasar sun bude rediyonsu jiya Lahadi da fatan za su ji abin da zai sa su yi murnar kawo karshen abin da ya kasance tsawon shekaru 37 na mulkin kama karya da Mugabe ya yi.

Sun yi matukar takaicin abin da ya faru, wasu ma har kuka su ka yi ta yi, bayan da su ka ji Mugabe ya ce shi ne ma zai jagoranci taron jam’iyyarsu ta ZANU-PF da za a yi watan gobe.

Jam’iyyarsu mai mulkin kasar ta bashi wa’adin zuwa yammacin yau Litini ya yi murabus ya kuma nada mataimakin Shugaban kasa da ya kora Emmerson Mnangawa a matsayin jagoran jam’iyyar.

Da babban kwamitin jam’iyyar ke daukar matsayi ya ce Chinamasa ya sauke Shugaban kasa daga manyan matsayi biyu na ZANU-PF:

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG