Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannan Al’ummomin Muhavul da Fulani sun Dauki Matakan Tsaro


Fulani makiyayi.

Bata gari ne suka haddasa rikicin da ya faru a karamar hukumar Mangu.

Shugabannnan al’ummomin Muhavul da Fulani a karamar hukumar Mangu dake jihar Plateau, sun dauki matakan gaggawa na dakile matsalar tsaro a yankin bayan wani tashin hankali da yayi sanadiyar rasa rayuka da dama da kuma dukiyoyin jama’a a wasu kauyuka a yankin.

A cewa shugaban karamar hukumar Mangu, Mr. Kaleb Mutfang, a yanzu haka hankali ya kwanta, kuma sun bukaci wadanda suka kaurace ma mahallansu da su koma. Kuma yace fadan da ya faru ba tsakanin Fulani da al’ummar Muhavul bane, wasu ‘yan tada zauna tsaye ne suka shigo gari don tada hankali.

Shi ma sakataren Myatti Allah a karamar hukumar ta Mangu, malam Tahiru Ummar yace Fulani da al’ummar magabul ‘yan uwan juna ne kuma tuni suka sasanta kansu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

XS
SM
MD
LG