Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Amurka da Rasha zasu mara wa Majalisar Dinkin Duniya baya domin warware rikicin Syria


Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump da na Rasha Vladimir Putin sun amince su goyi bayan Majalisar Dinkin Duniya domin a kawo karshen yakin basasan kasar Syria da yaki ci yaki cinyewa

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa Vladimir Putin sun amince su marawa Majalisar Dinkin Duniya, ko MDD baya, domin a kawo karshen yakin basasan Syria cikin lumana, wanda aka kwashe kusan shekaru bakwai ana yi.

Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce shugabannin biyu sun kwashe sama da sa’a guda suna tattaunawa, inda suka jaddada muhimmancin kawo karshen halin kakani-kayin da kasar ta shiga, inda miliyoyin ‘yan Syria suka rasa muhallansu.

Shugaba Trump da Putin sun ce akwai bukatar a bar mutanen kasar da suka tsere su koma gidajensu, sannan a tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasar ba tare da wata muguwar manufa ba, da kuma kawar da duk wata maboyar ‘yan ta’adda.

Shugaba Trump ya gana da takwaran aikin nasa ne ta waya talho, kwana guda bayan da shugaban Rashan ya tattauna da shugaban Syria Bashar al- Assad, kan yadda za a shawo kan yakin basasan kasar a siyasance, wanda ya lakume rayuka dubu 400.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG