Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin APC Na Jihohin Arewa 19 Sunyi Taron Goyawa Shugaba Buhari Baya A Abuja


ALI BUKAR DALORI, Shugaban APC na jihar Borno
ALI BUKAR DALORI, Shugaban APC na jihar Borno

Shugabannin jam'iyyar APC na jihohin arewa goma sha tara sunyi taron jaddada goyon bayansu ga Shugaba Muhammad Buhari a Abuja tare da yi masa godiya

Shugaban APC na jihar Borno Alhaji Ali Bukar Dalori shi ya zanta da Muryar Amurka inda ya bayyana makasudin taron da abubuwan da suka cimma.

Inji Alhaji Dalori su shugabannin APC na arewa gaba daya sun yi taro sun ga kuma ya kamata su mikawa shugaban kasa Muhammad Buhari godiyarsu tare da nuna masa goyon bayansu. Sun yi farin ciki da abubuwan da yayi, fatansu kuma shi ne Allah ya barshi ya kuma cigaba da yin ayyukan alheri.

Shugaba Buhari ya taimakawa mutanensu inji Alhaji Dalori kuma ya kawo tsaro abun da babu da. Buhari ya dukufa da kwato hakkin jama'a daga wadanda suka wawuresu saboda haka jama'a su tashi su taimaka masa.

Akan batun rashin lafiyar shugaban, Alhaji Dalori yace hutu ne ya je saboda siyasa ce 'yan adawa suka shigo da ita akan lafiyar shugaban.

Dangane da wasu matsaloli da suke kunno kai kamar karancin man fetur a wasu wurare Alhaji Dalori yace wadanda suka yi barna da can suke haddasa lamarin domin cimma muradunsu.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

XS
SM
MD
LG