Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin EU Sun Cimma Matsaya Kan Tallafin COVID-19


Wasu shugabbanin EU a yayin tattaunawa

Shugabannin kungiyar tarayyar turai ta EU sun cimma yarjejeniya ta kashe dalar Amurka triliyan 2.1 a matsayin kasafin kudin tallafin annobar coronavirus.

Yarjejeniyar ta hada har da dala biliyan 857 da za’a bayar a matsayin bashi da tallafi ga kasashen da suka fi galabaita sanadiyar coronavirus.

An cimma wannan matsaya ne bayan da aka kwashe kwanaki har hudu ana tattaunawa, fiye da yadda aka yi zato.

Dakin da shugabbanin suka tattauna a Belgium
Dakin da shugabbanin suka tattauna a Belgium

Abin da ya fi daukar hankali shine rarrabuwar kawuna da aka samu tsakanin kasashen da suka fi arziki da ke arewacin nahiyar da su ka hada da Netherlands da Austria, wadanda su ka nemi a rage ainihin kasafin kudin na dala biliyan 572 tare da gindaya sharruda masu tsauri na kashe su.

A waje daya kuma Spain da Italiya sun bukaci da a sassauta sharrudan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG