Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Fulanin Jihar Taraba Sun Yi Taron Shawo Kan Matsalolin Satar Shanu


Fulani makiyaya da shanunsu

Biyo bayan yawan satar shanu da satar mutane da sata da makami da suka addabi jihar da yadda duk wadanda aka kama matasan Fulani ne ya sa shugabanninsu suka shirya taron shawo kan lamarin

Duk wadanda aka kama da satar mutum, satar shanu da fashi da makami matasan Fulani ne.

Wani shugaban Fulanin yace abun da ya lura dashi shi ne su tsaya tsayin daka su dakile wadannan ayyukan asha da suka addabesu saboda sace sace da kashe kashe, duk wanda aka kama bafillatani ne.

Shanu a kasuwar Enugu
Shanu a kasuwar Enugu

Satar shanu da satar mutane domin samun fansa ya zama tamkar ruwan dare gama gari a jihar ta Taraba lamarin da ke sa mutanen jihar zaman dar dar.

Taron ya hada da makiyayan jihar da wasu ma daga waje domin lalubo bakin zaren matsalolin da suke fuskanta.

Muhammad Mafindi Umar Dan Buram mai ba shugaban kungiyar Miyetti Allah shawara akan harkokin kiwo kuma shugaban Miyetti Allah na jihar Taraba yace makasudin taron domin su duba abubuwan da suka shafesu suka zama masu illa a rayuwar bafillatani da nufi dakilesu.

Yace sun damu da yadda ake sace shanu da sace mutane da kuma fashi da makami. Ana sace mutane a boyesu sai an biya diya.

Yace taro ya yi kyau. Duk wakilan Fulanin jihohi goma sha shida dake Taraba sun hallara. Sun yadda yanzu su je su ja kunnuwan 'ya'yansu cewa dan bafullatani basu yadda ajishi a harakar sata ba.

Baicin hakan Fulanin zasu sa rana su raba goro su sauke Kur'ani ranar domin kawo karshen duk wani mugun hali na matasansu.

Shi kuwa Ardo Husseini Yusuf Boso mataimakin shugaban kungiyar Fulani ya yabawa jihar Taraba bisa yunkurin da suka yi.makiyaya. Yana fatan 'ya'yansu zasu ji tsoron Allah su bar sata da fashi da makami domin basu iske iyayensu cikin sata ba.

Ya kira gwamnatoci su wayar da kawunan Filani kuma su inganta ilimin yaran Fulani domin a samu sassauci a kasar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG