Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Hukumomin Leken Asiri Na Amurka Sun Amince Rasha Tayi Kutse A Zaben Kasar


Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dattawan Amurka

Shugabannin manyan hukumomin leken assirai na Amurka sunce sunyi imanin cewa Rasha ce ke da hannu dumu-dumu a cikin kutsen da aka yi da kuma bayyana asirin bayanan da aka tatso daga hanyoyin sadarwar duniyar gizo na jam’iyyar Democrats, kuma sunyi hakan ne don neman yin tasiri a wajen juya alkiblar zaben 2016 da aka kamalla.

A lokacinda suka bayyana jiya a gaban Kwamitin Harakokin Soja na Majalisar Dattawan Amurka, shugaban Hukumar Leken Assirai, James Clapper da shugaban Hukumar Tsaro Michael Rogers da kuma karamin sakataren ma’aikatar tsaron Amurka na Amurka Marcel Lettre, sun ce ra’ayinsu yazo daya akan cewa abinda suka kira “shugabannin kul da kul” na Rasha ne kawai ke da ikon bada iznin a yi irin wannan shisshigi da satar bayanai na asirin wata kasa.

Sun kuma bayyana abinda Rasha din tayi da cewa “barazana ce ga muradun” Amurka.

Sai dai kuma Clapper yace ba zasu iya auna tasirin aibin da bayanan da cibiyar Wikileakes ta sako akan zaben ba.

Shugaban Amurka mai bari gado Barack Obama ne ya umurci hukumomin leken assiran su bi diddigin duk shisshigin da ake jin wasu kasashen ketare sunyi a harakokin zabe, tun daga zaben da aka yi a shekarar 2008 har zuwa yau.

XS
SM
MD
LG