Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashe Biyar Na Afirka Ta Yamma Sun Yi Taro A Nijar


NIGER: Tarom wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka
NIGER: Tarom wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka

Shugabannin kasashen yammacin Afirka da suka hada da Nijar, Benin, Burkina Faso, Ivory Coast da Togo su ne suka hallara a Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar domin tattaunawa akan manufar kungiyar tasu.

Shugaban kasar Nijar wanda kuma shi ne shugaban kungiyar kasashen biyar shi ya bude taron da jawabi na musamma.

Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar yana jawabi a wurin taron kungiyar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar yana jawabi a wurin taron kungiyar

Wannan kungiyar dai an kafata ne a shekarar 1959 da nufin bunkasa tattalin arziki da bada damar zirga ziega ga al'ummomin kasashen.

Saidai yadda matsalar Boko Haram a Najeriya da rikicin azbinawan Mali suka ta'azara sun sa shugabannin kungiyar bada fifiko akan batun samar da tsaro.

A cewar ministan tsaron kasar Nijar Kanar Ibrahim Yakuba yace shugaban kasa yace sai an nemi dabaru da suke daidai da irin ta'adancin yanzu kafin a cimma nasara. Dalili ke nan ya bada shawarar kafa dakaru na musamman da zasu samu horon da ya yi daidai da halin da ake ciki yanzu.

Sun kafa irinta a kan iyaka da Najeriya da Chadi. Suna kuma neman izini su kafa wata a iyaka da Mali kodayake akwai sojojin kasashen duniya kusan dubu 15 amma Nijar bata samu saukin hare-haren 'yan Mali ba..

Kwararrun kasashen sun gabatar da muhimman shawarwari ga shugabannin wannan kungiya domin dorewar ayyukan da aka sa gaba.

Taron shugabannin kasashen yammacin Afirka
Taron shugabannin kasashen yammacin Afirka

Issoufou Isa, mataimakin sakataren zartaswa na kungiyar yace sun basu shawara akan abun da suke son yi, kamar gina manyan otel kowasu wuraren aiki da zasu kawowa kungiyar kudi.Zasu gina rijiyoyi domin bada ruwan sha da hanyoyi da kuma yin anfani da zafin rana domin samun wutar lantarki.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG