Accessibility links

Shugabannin kwarori a kano sun nesanta kansu daga makaman da aka kama a gidan wasu kwarori a birnin


Wasu makamai da aka kama a gidan wasu kwarori a birnin Kano

Shugabannin kwarori a Kano sun zanta da manema labarai game da makaman da aka kama a gidan wasu kwarori a birnin Kano.

Shugabannin kwarori a Kano sun zanta da manema labarai game da makaman da aka kama a gidan wasu kwarori a birnin Kano. Shugaban Kwarorin Tahir Fadalla ya nesanta kungiyarsu da makaman da aka kama. Ya ce kada mutane su dauka cewa haka duk kwarori su ke.

Ya ce sun dade a Kano. A Kano aka haifesu. Sun yi shekaru fiye da dari suna zaune a Kano. Ta dalilin haka ya ce Kano garinsu ne. Najeriya kuma kasarsu ce. Amma sun yarda a hukumta wadanda aka kama bisa ga shariar kasar.

Mahamud Ibrahim Kwari nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG