Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Rikon Jam'iyyar APC Sun yi Gangamin Karbar Atiku Abubakar


Gangamin Karbar Atiku Abubakar
Gangamin Karbar Atiku Abubakar

Shugabannin jam'iyyar APC na kasa sun dira kan birnin Yola inda suka hada gangamin karbar Atiku Abubakar wanda ya canza sheka daga PDP zuwa jam'iyyarsu.

Shugaban rikon jam'iyyar APC na kasa Chief Bisi Akande shi ya mikawa Atiku Abubakar tutar jam'iyyar lokacin gangamin da suka shirya a Yola babban birnin jihar Adamawa

Sun shirya gangamin ne domin karbar Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya wanda ya yiwa jam'iyyarsa ta PDP adabo ya koma APC. Yayin gagamin tsohon gwamnan Bayelsa Mr. Da Silva ya mika neman gafarar al'ummar Neja Delta bisa abun da ya kira kasawar da dansu ya yi. Ya ce a shekarar 2011 ya ziyarcesu tare da wasu gwamnoni arewa inda suka amince su zabi shugaba Goodluck Jonathan kuma suka yi hakan. Amma gashi ya kasa yin komi. Ya ce don haka al'ummar Neja Delta ta umuarceshi ya zo ya nemi gafararsu kuma ya tabbatar masu cewa zasu yi aiki da 'yan arewa a sabuwar jam'iyyar APC domin kawo canji da cigaban kasa.

Shi ma Atiku Abubakar ya yi karin haske game da dalilan da suka sa ya bar PDP. Ya ce na daya zasu kafa kwamitin riko na jam'iyyar. Na biyu su tabbatar cewa ranar Laraba wato gobe sun fito an yi masu ragista. Ya ce basu fara kemfen ba. Idan sun fara zasu ji jawabi daga wurinsa. Ya ce canji na zuwa kuma sai an yi canjin a Najeriya.

Gwamnan Adamawa Murtala Nyako ya ce yanzu an bude wani sabon babi a faggen siyasar jihar da na kasa. Idan Allah ya yarda zasu dakatar da zaluncin da a keyi a Abuja.

Amma Barrister A. T. Shehu sakataren jam'iyyar PDP a jihar Adamawa ya ce su basu damu da gangamin ba ko kuma ficewar Atiku Abubakar. Ya ce siyasa ta gaji shigowa da ficewa. Domin wani ya fita ko ya shigo ba zai sa ka ci zabe ba ko ka fadi zabe ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG