Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabar Hong Kong Ta Yi Nadamar Zangazangar Yan Kasarta


A wani al'amari mai kama da nuna nadama amma kuma tare da kin mika wuya ga masu zanga-zanga a kasar Hong Kong, Shugabar kasar Carrie Lam, ta yi takaicin aukuwar abin da ya kai ga zanga-zanga a kasar ba tare da biyan bukatar masu zanga-zangar kwata-kwata ba.

Shugabar Hong Kong mai goyon bayan China, Carrie Lam, ta bayar da hakuri jiya Talata game da rikicin siyasa da tashin hankalin da ya faru sakamakon wani kudurin doka da zai bada damar a dauki mai laifi zuwa kasar China domin yi masa shari’a. Amma ba ta amsa kiran masu zanga-zanga ba, na neman ta sauka daga mukaminta kan yadda ta tafiyar da lamarin kudurin dokar da ya janyo cece-kuce.

Lam ta fada wa manema labarai cewa an dakatar da aiki kan kudurin har sai lokacinsa ya kare a watan Yulin shekara mai zuwa, amma ta kuma sha alwashin tsayawa da kammala sauran wa’adinta a kan mulki.

“Na ji ku ‘karara kuma na yi dana sanin abin da ya faru,” a cewar Lam, ta kuma ‘kara da cewa ita da kanta ta dauki alhakin abin da ya faru akan kudurin dokar.

Facebook Forum

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG