Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabar Yankin Hong Kong Ta Dari Dari Da Matakin Amurka


Rigimar yankin Hong Kong

A wani al'amari mai kama da hanunka mai sanda ga Amurka da sauran kasashen duniya, Shugabar Hong Kong ta ce hawainiyar masu katsalandan ta kiyayi ramar Hong Kong.

Shugabar yankin Hong Kong Carrie Lam, ta yi kallon-hadarin-kaji, ga duk wani yunkuri da Majalisar Dokokin Amurka ke yi, na yin wata sabuwar doka da za ta shafi yankin.

“Gwamnatin wannan yanki, ta lura cewa wasu majalisun dokokin kasashen waje, musamman na Amurka, na shirin gabatar da wani kudurin doka, da zai yi katsalandan a harkokin Hong Kong, sam! ba za mu amince da wannan ba,” inji ta.

Kalaman na shugaba Carrie Lam, na zuwa ne, bayan zanga zangar da aka yi a ranar Lahadi, wacce dubban mutane suka yi tattaki zuwa ofishin jakadancin Amurka da ke birnin na Hong Kong, suka yi kira ga Amurkan da ta amince da wata dokar tabbatar da “’yancin bil Adama da da mulkin Dimokradiyya” da ta shafi yankin na Hong Kong.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG