Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sifaniya: An Haramta wa Rubiales Shiga Sha’anin Wasanni Tsawon Shekaru Uku


Rubiales
Rubiales

Tun a baya hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta haramta masa shiga sha’anin wasanni tsawon shekaru uku.

An haramtawa tsohon shugaban hukumar wasannin kasar Sifaniya shugabantar duk wani sha’anin wasanni tsawon shekaru uku a kasar.

Hukuncin da aka yanke wa Luis Rubiales na zuwa ne bayan da aka same shi da laifin sumbatar wata ‘yar wasan kasar ba tare da umarninta ba a gasar kofin mata ta duniya.

Jenni Hermoso
Jenni Hermoso

Tun a baya aka tilastawa Rubiales ya sauka a mukaminsa duk da yunkurin da ya yi na cijewa kan sumbatar ‘yar wasan Sifaniya Jenni Hermoso a bikin rufe gasar kofin duniya ta mata da Sifaniya ta lashe a ranar 20 ga watan Agusta a Australia.

Hukuncin na Rubiales na zuwa ne a ranar Juma’a wanda wata tawagar masu sa ido kan sha’anin wasannin a Sifaniya ta yanke.

Tun a baya hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta haramta masa shiga sha’anin wasanni tsawon shekaru uku.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG