Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar kasar Malawi


Galibin mutanen Malawi manoma ne

Wani madugun ‘yan adawa a Malawi na zarigin Shugaba Bingu Wa

Wani madugun ‘yan adawa a Malawi na zarigin Shugaba Bingu Wa Mutharika da tayar da husuma ta wajen umurtar mabiyansa su matukar kare shi daga hare-haren siyasa.

Humphrey Mvula, Mataimakin Shugaban jam’iyyar United Democrat, ya gaya wa Muryar Amurka cewa hurucin na Shugaban kasa baya bisa ka’ida, ya ce idan kasar ta fada cikin tashin hankalin siyasa to laifin Shugaban kasar ne.

A farkon wannan wata ne Shugaba Mutharika y ace yakamata magoya bayansa, a ta bakinsa, “su shigo cikin al’amarin don su kare babansu” daga cin mutuncin da masu bayar da tallafi na kasa da kasa da kungiyoyin rajin kare hakkoki ke masa, wadanda ya ke kuma zargi da tayar da fitina.

Shugaba Mutharika na kara shan matsin lamba kan ya sasanta takaddamarsa da masu bayar da tallafi na kasa da kasa, wadanda da yawansu su ka tsai da bayar da tallafi ga wannan kasa ta kudancin Afirka bayan munanan matakan murkushe masu zanga-zanga a cikin watan Yuli.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG