Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Snowden Na Kewar Amurka


Snowden
Snowden

​Wanda ake nema da laifi, kuma wanda ya kira kanshi dan leken asiri da ya tona asirin hukumar tattara bayanan sirrin Amurka, Edward Snowden yace yana so ya dawo gida Amurka.

A tattaunawar farko da yayi da gidan Talabijin din Amurka, Snowden ya gayawa dan jaridar NBC Brian Williams Larabannan cewa yana kallon kanshi a matsayin mai kishin kasa, kuma zai roki Rasha ta kara masa wa’adin fakewa a kasar kafin ya iya komowa Amurka.

Mr. Snowden yayi kokarin kare kanshi daga tuhume-tuhumen gwamnatin Obama dake cewa shi mai cin amanar kasa ne, wanda ya saka rayuka a cikin hadari saboda fallasa yadda hukumar da yayi wa aiki take leken asiri.
XS
SM
MD
LG