Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Najeriya Sun Kaddamar Da 'Operation A Watse' Kan Tsagerun Niger Delta


Wani Bangare Na Yankin Niger Delta a Najeriya

Ana nan har yanzu ana kik-kaka tsakanin gwamnatin Najeriya da tsagerun Neja Delta da ake kira da suna Avengers, wadanda ke ikirarin kare yankinsu mai arzikin man fetur. Wannan ce tasa rundunar sojin Najeriya ta kafa shirin da ta Kira da suna ‘Operation a Watse’.

A yan tsakanin nan rahotannin na nuna cewa wadannan tsagera suna kaiwa jama’a a wasu sassan kasar farmaki tare da barnata bututun man fetur da kamfanonin hakar danyen mai.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar ya bayyana dalilan da yasa suka fatattaki ‘yan ta’addar Naija Delta da ke barnata dukiyar kasa da kuma al’ummar da suke hallakawa ko jikkatawa.

Sojan ya bayyana cewa sun kai farmakin sun kuma yi nasara a tashin farkon nan. Inda suka tarwatsa na tarwatsawa da kum aci gaba da fakon masu alaka da wadannan bata garin mutane da sunan fafutuka.

Game da cewa wai an ritsa da farar hula a wajen kai farmakin ga tsageran Neja Delta, Rabe yace duk farfaganda ce kawai daga su tsageran don a ce soji na hallaka farar hula.

A karshe dakaren yayi kira ga al’ummar Najeriya da su daure su dinga taimakawa jami’an tsaro da rahoton duk wata makwantar tsageran da ke kawo tarnaki ga tsar da kwanciyar hankalin Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG