Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Na cikin Wadanda Aka Kama Suna Fashi da Makami da Sace Mutane


Wasu cikin barayi masu fashi da makami da sace mutane da Ali Kwara yayi sanadiyar cafkesu

Bincike ya nuna cewa mutanen da aka kama akwai sojoji a cikinsu kuma su ne suke yawancin fashi da makami da sace mutane da fasa kantuna da sayarda man fetur a kusan duka jihohin arewacin Najeriya.

Alhaji Ali Kwara shi ya yiwa 'yan jarida bayani kan irin aikin ta'adancin da mutanen ke aiwatawa.

Yace wadanda da aka kama suna sace mutane suna kuma fashi. Kwanan nan suka sace wani dan'uwan Nuhu Ribadu mai suna Sani Ribadu, inji Ali Kwara. Kudin da suka karba hannunsa sun kai nera miliyan goma sha biyar.

A wata karamar hukuma a jihar Adamaa barayin sun kwace albashin ma'aikata da suka kai nera miliyan ishirin. Akwai wani dan majalisar jihar da suka karbi nera miliyan bakwai a hannunsa. Haka ma suka yiwa wani sirikin Atiku a Jada. A gidajen mai dake Gurore har manajan gidan mai suka kashe.

Ali Kwara ya kama barayi masu fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane suna karban kudin fansa
Ali Kwara ya kama barayi masu fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane suna karban kudin fansa

Mutanen suna fashi a hanya daga Yola zuwa Jalingo. Haka ma ta wajen Gombe zuwa Kumo suna fashi suna sace mutane. Cikin garin Gombe ma suna fashi. Gungun kungiyarsu ita ce tafi kowace kwarewa a fashi da makami a Najeriya a cewar Alhaji Ali Kwara tare da kara da cewa tunda ya fara aikinsa bai taba ganin kungiya irin tasu ba.

Akan yadda mahukuntan Najeriya ke saurin sako bata garin da shi Ali Kwara ya kama ba tare da hukumtasu ba sai yace 'yan Najeriya sun san inda matsalar take tunda yanzu an soma dago masu shari'a. Yace tunda Najeriya take bata taba daukar hanyar gyara ba sai yanzu. Yace duk matsalar Najeriya shari'a ce. Yace duka kashe-kashen da ake yi a kasar shari'a ce babu. Rashin shari'a shi ya kawo duk fadan da ake yi, inji Alhaji Ali Kwara.

Ali Kwara ya tabbatar da sojoji na cikin wadanda aka kama. Yace Buratai ne ya kamasu da tarkon shi Ali Kwara. A irin fashin da 'yansanda keyi Ali Kwara ya gano sojoji ne ke basu kayan aiki. Sojoji na dauko mutanensu daga jihar Yobe suna kaiwa Tivi 'yan banga. Yace suna raba yara zuwa Niger, Kebbi, Sokoto da sauran wurare a arewa domin yin aika-aika. Ya gano duk shirinsu ya kuma dana tarko, Janar Buratai kuma ya bi sawu ya kamasu.

Wasu mutanen da aka kama sun amsa laifukansu. Wani Saji Manjo yace shi sata ya keyi. Suna fashi ne a Adamawa. Su ne suka kama Gombi. Shi ma Atiku Ibrahim wanda yace yana da gidaje a Numan da Jalingo yace suna sace mutane tare da yin fashi da makami. Su ne suka sace dan majalisa daga Kango. Bayan haka sun shiga gidan Maina Gurore sun yi barna. Su kan kuma tare hanya tsakanin Numan da Jalingo.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG