Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kashe Dan Sheikh Ibrahim Zakzaky da Wasu Mutane 10 a Zaria


Sheikh Ibrahim Zakzaky

Rahotanni daga Najeriya na fadin cewa sojoji sun bude wuta a kan masu gangamin Ranar Qudus a Zaria.

Rahotanni daga Najeriya na fadin cewa sojoji sun bude wuta a kan masu gangamin Ranar Qudus a Zaria, Jihar Kaduna, suka kashe mutane 11, cikinsu har da dan jagoran Kungiyar 'Yan'uwa Musulmi, Sheikh Ibrahim el-Zakzaky.

Ba a san dalilin da ya sa sojojin suka bude wuta kan wadannan masu zanga-zangar da suka saba yin irinta kowace shekara a ranar 25 ga watan Yuli ba.

Rahotanni daga Zaria na cewa an harbe aka kashe Mahmud Zakzaky tare da wasu mutanen su 10, cikinsu har da wata mace mai goyo a bayanta.

Musulmi 'yan mazhabin Shi'a su na gudanar da gangamin Ranar Qudus a kowace shekara a fadin duniya, domin nuna goyon bayansu tare da jajantawa Falasdinawa dake karkashin mamayar kasar Isra'ila.

A bayan Zaria ma, an gudanar da irin wannan gangami a manyan birane da dama na Najeriya ba tare da samun tashin hankali ba.

Har ya zuwa yanzu ba a ji ta bakin hukumomin soja ko jami'an gwamnatin Najeriya a kan wannan lamarin ba.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG